Isa ga babban shafi

An samu nasarar kawar da cutar Marburg a Equatorial Guinea - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce an kawo karshen cutar Marburg a Equatorial Guinea, bayan da aka cika kwanaki 42 ba tare da an samu wanda ya harbu da cutar da ake yiwa lakabi da kanwar Ebola.

WHO ta yabawa jami'an kiwon lafiya da suka taimaka wajen kawar da cutar mai saurin yaduwa da kuma barazana ga rayuwar dan adam.
WHO ta yabawa jami'an kiwon lafiya da suka taimaka wajen kawar da cutar mai saurin yaduwa da kuma barazana ga rayuwar dan adam. AP - Bui Cuong Quyet
Talla

Masana kiwon lafiya sun bayyana cutar a matsayin babbar barazana da ke sanyawa dan adam tsananin zazzabi, zubar jinni da kuma yin illa ga sassan jikin mutum.

A ranar 13 ga watan Fabrairu ne, aka bayyana cutar a matsayin annoba a Equatorial Guinea, karon farko da kasar ta taba irin wannan cuta a kasar da ke Tsakiya maso Yammacin Afirka.

Mutum 17 aka tabbatar sun harbu da cutar, yayin da 12 suka mutu. Amma WHO ta ce dukkanin mutum 23 da aka gano sun mutu.

Sanarwar da WHO ta fitar, ta yabawa jami’an lafiya da sauran kungiyoyi na hadin gwiwa da suka taimaka wajen kawar da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.