Shugaban Saliyo da 'yan takara 12 za su fafata a zaben Asabar
Al'umman kasar Saliyo suna shirin zuwa rumfunan zabe a karshen wannan mako domin zaben shugban kasa, zaben za’a fafata tsakanin 'yan takara 13, ciki har da shugaban kasar mai ci.
Wallafawa ranar:
Shugaba Julius Leones Maada Bio mai shjekaru 59, wanda yake neman a sake zabensa a wani sabon wa'adi, yayi kira da a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Sai dai yana fuskanatar barazana daga jam’iyar Adawar kasar APC, wadda Dr. Samura Mathew Wilson ke yi mata takara..
Ko a zaben da aka gudanar a kasar a shekarar 2018, da kyar da jibin goshi shugaban mai ci ya kai bantensa a hannun Dr. Samura Mathew Wilson.
Doctor Samura Mathew ya kasan tsohon ministan harkokin wajen kasar a 2012, kana ya kuma rike ministan kudi da tattalin arziki a shekarar 2017.
Karo na biyar kenan da za agudanar da zaben shugaaban kasa a Saliyo tun bayan da aka kawo karshen yakin basasa da aka yi a kasar daga shekarar 1991 zuwa 2002, yakin da ya lakume rayukan mutane dubu 50, ya kuma haddasa asarar dubban gidaje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu