Isa ga babban shafi

Al’ummar Saliyo na shirin kada kuri'a a babban zaben kasar

Al’ummar Saliyo na shirin fita rumfunan zabe a gobe Asabar don kada kuri’a a babban zaben kasar da ‘yan takarar shugaban kasa 13 za su fafata ciki har da shugaba mai ci Julius Maada Bio wanda ke neman wa’adi na biyu a mulkin kasar. 

Masu sa ido kan zaben Saliyo.
Masu sa ido kan zaben Saliyo. © Yemi Osinbajo
Talla

 

Akalla al’ummar Saliyo Miliyan 3 da dubu 400 ake sa ran su kada kuri’a a zaben na gobe asabar wanda ke zuwa dai dai lokacin da kasar ke ganin matsanancin koma bayan tattalin arziki. 

Shugaba Julius Maada Bio wanda ke neman wa’adi na 2 na fuskantar babban kalubale daga babban abokin adawarsa Samura Kamara wanda dama da shi ne suka fafata a zaben 2018 wanda shugaban ya lashe, sai kuma karin ‘yan takara 11 ciki har da mace guda wadanda dukkaninsu ke neman kujerar shugabancin kasar ta Saliyo. 

Zaben na gobe asabar wanda ya kunshi, hadda na ‘yan majalisun tarayyar da kuma shugabannin yankunan kasar, akwai fargabar tashe-tashen hankula bayan da manyan jam’iyyun adawa ke ci gaba da zargin juna da shirin kitsa rikici, lamarin da ya tilasta tsanantar kiraye-kirayen ganin al’umma basu shiga rikici ba. 

A kwanankin baya-bayan nan dai anga yadda kaiwa juna farmaki tsakanin magoya bayan shugaba mai ci Maada Bio da kuma jagoran adawa Samura ke ci gaba da tsananta.  

Bangaren adawa na ci gaba da dora alhakin tabarbarewar tattalin arzikin kasar kan shugaba mai ci yayinda dan takara Samura ke nanata kudirinsa na samar da gagarumin sauyi a kasar wadda al’ummarta ke ci gaba da ganin matsin rayuwa da hauhawar farashin kayaki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.