Aljeriya ta tisa keyar yan ci ranin kasashen Afrika sama da dubu 9 a jamhuriyar Nijer
Rahoton wasu hukumommin majalisar dinkin duniya biyu ya ce Algeria ta tisa keyar bakin-haure ‘yan Afrika sama da dubu 9 daga iyakarta zuwa Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya haddasa mummunar matsalar jinkai.
Wallafawa ranar:
A cikin rahoton, hukumar kula da ayyukan jinkai ta OCHA da ta kula da bakin haure sun ce tun daga farkon wannan shekarar ce mahukuntan Algeria suka kori wannan adadi na bakin haure, inda suka makale a wani gari da ake kira Assamaka da ke jihar Agadez.
Mahukuntan Nijar sun yi wa sama da mutane dubu 9 da ke shigowa rajista, cikinsu maza dubu 8 da dari 8 da 28, mata 161, yara maza 152 da yara mata 51 tun dvaga watan Janairu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu