Isa ga babban shafi

Mutane da dama sun fito don kada kuri'a a babban zaben kasar Saliyo

Al'ummar kasar Saliyo sun kada kuri'a a babban zaben kasar da aka gudanar cikin lumana, sai dai an samu jinkirin fara kada kuri’ar a wasu rumfunan zabe, ya yin da 'yan adawa suka yi Allah wadai da kura-kurai da ake zargin an tafka a zaben.

Yadda masu kada kuria suka hau layi don jefa kuri'ar su a babban zaben kasar Saliyo.
Yadda masu kada kuria suka hau layi don jefa kuri'ar su a babban zaben kasar Saliyo. REUTERS - COOPER INVEEN
Talla

Shugaban kasar mai ci Julius Maada Bio na neman wa’adi na biyu, duk kuwa da tsadar rayuwar da al’ummar kasar ke fuskanta da ya haifar da boyen da aka samu asarar rayuka a kasar a shekarar da ta gabata.

‘Yan takara 13 ne suka fafata a zaben daga ciki kuma akwai Mace daya, sai dai ana ganin dan takarar jam’iyar adawa ta APC Samura Kamara ne babban abokin hamayyar Bio.

Bayan kada kuri’arsa a barikin Wilberforce da ke birnin Freetown, shugaba Bio ya bukaci al’ummar kasar da su fito su jefa kuri’a cikin lumana, sannan su gudanar da shagulgulan samun nasara ba tare da rikici ba.

Sai dai sakataren jam’iyar adawa ta APC Lansana Dumbuya, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, tsaikon da aka samu a iya yankunan da jam’iyar su ke da karfi ne, ya yinda aka fara jefa kuri’a da wuri da jam’iyar mai mulki ta SLPP ke da karfi.

Kamfanin dillancin labarai na APF ya ruwaito cewar, wani jami’in soja da wakilan sa suka samu a wata rumfa a birnin Freetown, ya tabbatar musu sai karfe biyu na rana agogon kasar aka fara zabe a rumfar, wanda ya sabawa ka’idar fara zaben kasar, da aka shirya farawa da karfe 7 na safe a kuma kammala karfe 5.

A sanarwar da gamayyar kungiyoyin fararen hular cikin kasar da suke sanya ido kan zaben, sun ce kashi 84 na rumfunar zaben da suka kewaya a fadin kasar, da karfe 8 na safiya aka fara kada kuri’a, haka nan kaso 59 na rumfunan zaben da ke birnin Freetown ne kadan aka fara zabe a kan lokaci.

Rahotanni sun nuna cewar an samu fitowar masu kada kuri'a da dama a lokacin zaben, inda yanzu al'ummar kasar ke dakon fara fitowar sakamakon zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.