Isa ga babban shafi

Jam'iyar shugaba Bio ta samu rinjaye a majalisar dokokin Saliyo

Jam’iyar mai mulki a Saliyo ta samu nasarar lashe kashi 60 na kujerun majalisar dokokin kasar, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar a jiya asabar, wanda kuma ke zuwa a dai-dai lokacin da jam’iyar adawa ke bukatar gudanar da zagaye na biyu a zaben da shugaba Julius Maad Bio ya lashe.

Shugaban kasar Julius Maada Bio, da jam'iyarsa ta samu rinjaye a majalisar dokokin kasar.
Shugaban kasar Julius Maada Bio, da jam'iyarsa ta samu rinjaye a majalisar dokokin kasar. REUTERS - COOPER INVEEN
Talla

A cewar sakamakon zaben da shugaban hukumar Mohamed Kenewui Konneh ya karanto, jam’iyar SLPP da ke mulki ta samu nasarar lashe kujeru 81, ya yinda jam’iyar adawa ta APC ta lashe kujeru 54.

Sakamakon ya nuna cewar jam’iyar SLPP ta yi nasarar lashe kujeru 7 daga cikin 10 da ake da su a gundumar Kono inda a baya batada ko daya, haka nan a yankunan arewaci da kuma yammaci, musammama babban birnin kasar Freetown wanda ke zaman ci biyar jam’iyar adawa, SLPP ta taka rawar gani.

Jam’iyar APC da tun da farko taki amincewa da sakamakon zaben sabida zargin tabka kurakurai a wasu wurare, har yanzu ita ce ke rike da kujerar magajin garin Freetown, bayan samun samada kashi 51 na kuri’un da aka kada. 

Haka nan jam’iyar APC ta ce ba za ta shiga cikin gwamnatin ba, sabida zargin magudin da aka samu a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.