Isa ga babban shafi

An kama wani mutum da laifin kisan mutane sama da 10 a Rwanda

An kama wani mutum da ake zargi da aikata kisan gilla bayan gano gawarwaki fiye da 10 a cikin wani rami da aka tona a dakin girkin da ke gidansa na Kigali, kamar yadda 'yan sanda da kafofin yada labarai na kasar Rwanda suka ruwaito.

Mutumin ana zargin sa da kashe mata da maza da yake yaudarar su zuwa gidansa.
Mutumin ana zargin sa da kashe mata da maza da yake yaudarar su zuwa gidansa. © AFP
Talla

'Yan sanda sun ce wanda ake zargin mai shekaru 34 da haihuwa ya gamu da wadanda abin ya shafa maza da mata a cikin mashaya inda ya kai su masaukinsa na haya da ke wajen babban birnin Rwanda.

Kafofin yada labaran Rwanda sun yi ikirarin cewa an gano gawarwaki fiye da 10, kuma wata majiya ta shaida wa AFP, cewa ya zuwa yanzu gawawwaki 14 aka samu a gida nasa.

Tun a watan Yuli aka cafke mutumin bisa zargin sa da aikata fashi da makami da kuma laifin fyade, amma kuma an bayar da belinsa bisa rashin cikakkun hujjoji kan tuhumar da ake masa, in ji kakakin 'yan sandan yankin Thierry murangira.

Hukumomin kasar sun ce an ci gaba da gudanar da bincike duk da haka, abin da ya taimaka a gano aika-aikar da ya yi a wani dakin girki da ke cikin gidan nasa na birnin Kigali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.