Isa ga babban shafi

Rasha za ta gina wa Burkina Faso cibiyar sarrafa makamashin nukiliya

Gwamnatin Burkina Faso ta kulla yarjejeniya da kasar Rasha domin gina mata tashar sarrafa makamashin nukiliya, lamarin da zai kawo karshen karancin lantarkin da kasar da ke fuskanta.

Shugaban Rasha Vladimir Putin bayan karbar bakuncin shugaban mulkin sojan Burkina faso Ibrahim Traore a birnin Saint Petersburg.
Shugaban Rasha Vladimir Putin bayan karbar bakuncin shugaban mulkin sojan Burkina faso Ibrahim Traore a birnin Saint Petersburg. via REUTERS - TASS
Talla

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ce a birnin Moscow, yayin bikin da ya samu halartar ministan makamashi na Burkina Faso Simon-Pierre Boussim da Nikolay Spassky mataimakin daraktan hukumar makamashin nukiliya ta Rasha.

Alkaluman Bankin raya kasashen Afirka sun nuna cewa zuwa karshen shekarar 2020, kashi 23 cikin 100 ne kawai na al’ummar Burkina Faso ke samun wutar lantarki.

Kaso mai tsoka kuma na lantarkin da kasar ke amfani da ita, tana saye ne daga Ivory Coast da Ghana, yayin da take samar da wani kason wutar ta hanyar ruwa ko hasken rana.

Tashar da ake shirin ginawa Burkina Faso za ta zama ta biyu a Afirka, bayan guda daya tilo da yanzu ake da ita a nahiyar, wadda ke kusa da birnin Cape Town a Afirka ta Kudu.

Kasar Burkina Faso da ta kasance karkashin mulkin soja tun a shekarar da ta gabata, na ci gaba da karkata zuwa ga Rasha, bayan yin watsi da tsaffin abokanta na yammacin Turai, ciki har da ytsohuwar uwargijiyarta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.