Isa ga babban shafi

Adadin iyalan da ke cikin tsananin yunwa a Sudan ya rubanya - WHO

Wata sanarwar hadin gwiwa da WHO da kuma UNICEF suka fitar, ta ce adadin iyalan da ke fama da yunwa ya kusan rubanya a cikin shekarar da ta gabata a Sudan, inda yaki tsakanin janar-janar ya jefa kasar cikin rudani na tsawon watanni shida.

Yadda kaasuwar El Geneina da ke Darfur kenan ta koma.
Yadda kaasuwar El Geneina da ke Darfur kenan ta koma. © AFP
Talla

Rikicin ya kashe sama da mutane 9,000, ya kuma tilastawa miliyoyi barin matsugunansu, lamarin da ke kara ta'azzara matsalar rashin kwanciyar hankali a kasar, inda fiye da rabin mazauna yankuna da dama ke bukatar agaji.

A cewar WHO da UNICEF, yawan iyalan da ke fama da yunwa ya kusan rubanya a cikin shekarar da ta gabata.

Yara 700,000 na fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki inda 100,000 daga cikin su ke bukatar agajin gaggawa saboda matsanancin rashin abinci mai gina jiki tare da matsalolin lafiya.

Fiye da mutane miliyan 20.3, ko fiye da kashi 42% na al'ummar kasar, suna fuskantar matsanancin karancin abinci kuma wannan lamari ne na musamman a yankunan da ake fama da rikici, musamman a Darfur, Khartoum, Kudancin Kordofan, da kuma yammacin Kordofan, in ji shi kakakin UNICEF.

Yakin ya barke ne a ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin sojojin da ke karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhane da kuma dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da ke karkashin ikon Janar Mohamed Hamdane Daglo.

Sanarwar ta ce, sama da mutane miliyan 7.1 da suka rasa matsugunansu, ciki har da miliyan 4.5 da tun farkon rikicin Sudan suka rasa matsugunansu.

Miliyoyin yara ne ke kamuwa da cututtuka daban-daban, kamar su kwalara, zazzabin dengue, kyanda, da kuma zazzabin cizon sauro, yayin da tsarin kiwon lafiya ke fama da matsalar hare-hare, in ji hukumar WHO da Unicef.

Cutar kwalara, mai saurin yaduwa, ta kashe mutane 65, yawancinsu yara ne, inda ake fargabar hakan zai yi sanadiyar mutuwar mutane da dama idan ba a gaggauta shawo kan cutar ba, in ji kungiyoyin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.