Kungiyar Turai ta ba da motocin sulke 100 ga kasar Ghana
Ghana ta karbi sama da motoci 100 masu sulke daga kungiyar Tarayyar Turai, wadanda ke kara ba da taimako ga kasashen yammacin Afirka da ke fuskantar barazanar yaduwar hare-haren masu jihadi.
Wallafawa ranar:
Kasashe da dama a mashigin tekun Guinea da suka hada da Togo, Benin da Ivory Coast sun sha fama da hare-hare a yankunan kan iyaka da suka danganta da masu jihadi, yayin da Ghana ta kara yawan sojojinta a kan iyakarta ta arewa.
Motoci 105 masu sulke da aka kai Ghana a jiya Asabar, Josep Borrell bayan wata ganawa da shugaban Ghana Nana Akufo -Addo a Accra ya bayyana cewa za a yi musu karin kayan aikin sa ido ta sama da na’urorin yaki na zamani .
"Yaɗuwar rashin tsaro daga Sahel zuwa ƙasashen yankin Guinea ba abin tsoro ba ne. Abin takaici, a cewar Joseph Borrell.
Ya kara da cewa tallafin na Turai zai kuma shafi samar da ayyukan yi, musamman a arewacin kasar inda aka gano rikicin kabilanci da rashin aikin yi a matsayin hanyar da kungiyoyin masu dauke da makamai ke amfani da ita wajen daukar matasa.
Kungiyar ta EU ta bayyana cewa tallafin da za ta baiwa Ghana wani bangare ne na kudi Euro miliyan 616 da aka yi niyyar karfafa tsaron wadannan kasashe hudu na gabar mashigin tekun Guinea.
A farkon wannan shekara ne gwamnatin Ghana ta tura karin sojoji da 'yan sanda 1,000 zuwa yankin Bawku da ke arewacin kasar mai iyaka da Burkina Faso.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu