Isa ga babban shafi

An kafa dokar hana fita a Saliyo bayan kai hari barikin soji

Afirka – Gwamnatin kasar Saliyo ta kafa dokar hana fita a fadin kasar sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai rumbun aje makamai dake barikin sojin Freetown, abinda ya haifar da musayar wuta.

Shugaban Saliyo Julius Maada Bio
Shugaban Saliyo Julius Maada Bio REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Shaidun gani da ido sun shiadawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, sun ji karar harbe harbe da kuma fashewar wani abu mai karfi a yankin Wilberforce, inda rumbun aje makaman yake, kusa da ofisoshin jakadancin kasashen ketare.

Wasu shaidun sun ce sun ji karar musayar wuta kusa da barikin sojin dake unguwar Murray Town, dake dauke da sansanin sojin ruwan kasar da kuma wani sansanin sojin dake wani bangare na Freetown.

Wani faifan bidiyon da aka sanya a kafofin sada zumunta ya nuna wasu mutane a kan titunan kasar da aka ce sun gudu ne daga gidan yari bayan harin, amma kamfanin dillancin labaran Faransa bai iya tantance wanda ya bude musu kofar fita ba.

Magoya bayan Julius Maada bayan nasarar zaben da ya samu
Magoya bayan Julius Maada bayan nasarar zaben da ya samu AP - Cooper Inveen

Rahotanni sun ce an yi amfani da manyan makamai masu sarrafa kansu da kuma fashe fashe masu karfi kamar yadda aka dinga yadawa a kafofin sada zumunta.

Shaidun sun ce wannan ya sa mutane suka kauracewa titunan birnin Freetown domin komawa cikin gidajensu don kare lafiyarsu.

Wata da ake kira Susan Kargbo tace karar bindigogi da fashe fashen da taji ne daga barikin sojin Wilberforce suka tashe ta daga barci da misalin karfe 4.30 na safiyar yau.

Kargbo tace ta kadu sosai, yayin da harbe harben suka ci gaba har zuwa wayewar garin yau lahadi.

Sanarwar gwamnati tace sojoji sun yi nasarar murkushe wadanda suka yi kokarin fasa rumbun aje makaman, yayin da aka bukaci jama’a su zauna a cikin gidajen su.

Shugaba Julius Maada Bio tare da shugaban China Xi Jinping lokacin taro a Beijing
Shugaba Julius Maada Bio tare da shugaban China Xi Jinping lokacin taro a Beijing POOL/AFP

Ministan yada labarai Chemor Bah ya shaidawa jama’a cewar gwamnati da kuma rundunar sojin kasar sun tashi tsaye wajen tabbatar da tsaron lafiyarsu, yayin da ya kara da cewa domin bai wa jami’an tsaro damar farautar ‘yan bindigar da suka kai harin, an umurci jama’a da su zauna a gidajensu, yayin da aka saka dokar hana fita.

Babu wani karin haske a kan wadanda suka kai harin da kuma dalilin daukar matakin.

Yankin Afirka ta Yamma na fuskantar matsalolin juyin mulki tun daga watan Agustan shekarar 2020, ganin yadda kasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar da kuma Guinea wadda ke da iyaka da Saliyo suka gamu da juyin mulkin soji.

Shugaban Kasar Saliyo Juluis Maada Bio ya bi sahun jami’an gwamnatinsa wajen kwantar da hankalin jama’a cewar hankali ya kwanta a birnin Freetown, tare da bukatar mutane su zauna cikin gidajensu.

Bio yace yayin da hadin gwuiwar hukumomin tsaron kasar ke farautar wadanda suka kai harin, an kafa dokar hana fita a kasar baki daya, tare da bukatar ganin jama’a sun zauna cikin gidajensu.

Shugaban ya sake jaddada cewar gwamnati zata ci gaba da samar da tsaro da kuma kare lafiyar al’ummar kasar daga barazanarwadanda basa son zaman lafiya.

Ofishin jakadancin Amurka dake Freetown ya yi Allah wadai da yunkurin kai hari rumbun aje makaman, yayin da ya sha alwashin taimakawa wajen aiki da dimokiradiya da kuma zaman lafiyar Saliyo.

An dai zabi shugaba Maada Bio ne a shekarar 2018, yayin da a watan Yunin bana ya samu nasarar wa’adi na biyu da kuri’u sama da kashi 56 da aka kada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.