Isa ga babban shafi

Kasashen Mali da Burkina da Nijar na ci gaba da yunkurinsu na samar da tarayya

Ministocin harkokin kasashen wajen Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar da ke karkashin mulkin soji, sun amince da kafa kungiya a matsayin wani bangare na da dadden burinsu na hada kan kasashen da ke yammacin Afirka a matsayin tarayya.

Ministocin harkokin wajen kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar.
Ministocin harkokin wajen kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar. © Bureau de l’Information et de la Presse du ministère des Affaires étrangères
Talla

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar bayan wani taron kwanaki biyu da suka yi a Bamako babban birnin kasar Mali, ministocin harkokin wajen kasashen sun tattauna kan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da karfafa harkokin diflomasiyyarsu da ci gaban tattalin arziki da kuma kawancen siyasa.

Yarjejeniyar da kasashen suka cimma a tsakaninsu, ta kasan ce yunkurin da sukeyi na samar da hadakar tattalin arziki da kuma tsaro.

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop, ya ce za su mika wa shugabanninsu da za su gudanar da taro a Bamako a wani lokaci nan gaba, matsayar da suka cimma don yin bitarta.

Sanarwar ta ce ko a watan da ya gabata, sai da ministocin kasashen suka amince da tsarin tattalin arziki na bai daya da samar da bankin kasuwanci don samar da dai-daiton tattalin arzkinsu.

Mali da Burkina Faso da akayi juyin mulki a cikinsu a shekarun 2020 da kuma 2022, sun goyi bayan sojojin da suka yiwa shugaban Nijar Mohamed Bazoum juyin mulkin a watan Yulin da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.