Isa ga babban shafi

Tsohon Shugaban Kasar Saliyo zai amsa tambayoyi kan yunkurin juyin mulki

Hukumomin Saliyo sun sanar da aike wa tsohon Shugaban Kasar Ernest Bai Koroma sammaci, domin yi masa tambayoyi a game da hare haren baya bayan na da aka yi ta kaiwa da nufin yin juyin mulkin da ba a yi nasara a kai ba.

Tsohon Shugaban Kasar Saliyo Ernest Bai Koroma
Tsohon Shugaban Kasar Saliyo Ernest Bai Koroma © Michèle Spatari / AFP
Talla

Tun a ranar 26 ga watan jiya ne ‘yan sandan Kasar suka bukaci tsohon shugaban da ya mulki Kasar ta Saliyo dake yammacin Afrika na tsawon shekaru 11,  Shalkwatarsu  dake birnin freetown domin yi masa tambayoyi na musamman, kamar yadda Ministan yada labarun Kasar Cherno Bah  ya sanar .

Sammacin da aka aikawa tsohon Shugaban Kasar na zuwa ne bayan kama tsohon mai ba shi tsaro.

A cikin watan da ya gabata ne gomman ‘yan bindiga suka kai hari a barikokin soji dake birnin Freetown, da gidajen yari, inda suka kashe jami’an tsaro da dama suka kuma yi sanadiyar tserewar fursunoni sama da dubu 2, ko da yake an yi nasarar cafke mutane sama da 50 da ake zargi da hannu a hare haren, cikinsu akwai jami’an sojoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.