Isa ga babban shafi

Al'amura sun daidaita a Saliyo bayan yunkurin kifar da gwamnati

Gwamnatin Saliyo ta sanar da daidaituwar lamurra a babban birnin kasar Freetown bayan harin da aka kai kan manyan barikokin sojin kasar da gidajen yari a jiya Lahadi lamarin da ya kai ga sanya dokar takaita zirga-zirga ta sa’o’i 24.

Wani yanki na birnin Freetown gab da inda 'yan bindiga suka kai farmaki a yunkurin kifar da gwamnatin kasar.
Wani yanki na birnin Freetown gab da inda 'yan bindiga suka kai farmaki a yunkurin kifar da gwamnatin kasar. AFP - SAIDU BAH
Talla

Harin na sanyin safiyar jiya Lahadi ya tayar da hankulan jama’ar kasar ta yammacin Afrika bayan da aka shiga fargabar yiwuwar fuskantar juyin mulki.

A jawabin da shugaba Julius Maada Bio ya gabatar game da harin, ya ce tuni aka kame kaso mai yawa na mutanen da suka kitsa hare-haren kuma tuni hankula suka kwanta bayan kawar da duk wata fargaba.

Al’ummar birnin Freetown sun wayi gari da harbe-harben bindiga a jiya Lahadi bayan da wasu rike da makamai suka yi yunkurin kutsa kai cikin babban barikin sojin kasar da ke gab da fadar shugaban kasa.

Rahotanni sun ce an yi musayar wuta na tsawon lokaci tsakanin jami’an tsaron kasar da maharani da ke rike da makaman wadanda suka balle babban gidan yarin da ke rike da fursunoni fiye da dubu 2.

Wasu faifan bidiyo sun nuna yadda fursunoni ke tserewa kan tituna don guduwa daga inda suke a tsare.

 Shugaban kasar ta Saliyo Maada Bio ya ce, duk da nasarar shawo kan matsalar dokar takaita zirga-zirga za ta ci gaba da aiki daga kowacce karfe 9 na dare zuwa 6 na Safiya har sai al’amura sun kamala gyaruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.