Isa ga babban shafi

Amurka zata taimaka wa yammacin Afrika da dala miliyan 45 don yaki da ta'addanci

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana Shirin kasarsa na taimakawa yammacin Africa da dala miliyan 45 don yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaro.

Blinken na ziyarar wasu kasashen yammacin Africa don karfafa alakar da ke tsakanin Amurka da kasashen
Blinken na ziyarar wasu kasashen yammacin Africa don karfafa alakar da ke tsakanin Amurka da kasashen AP - Andrew Caballero-Reynolds
Talla

Blinken na wadannan kalamai ne lokacin da yake Shirin ganawa da shugabannin kasashen Najeriya, Cape Verde da Angola , a ziyarar kasashen Nahiyar Africa da ya fara ranar 21-26 ga watan da muke ciki na Janairu.

 

Manufar ziyarar dai itace tattauna alaka musamman ta kasuwanci tsakanin Amurka da kasashen yammacin Africa, sauyin yanayi, lafiya,tsaro da sauran matsaloli.

 

Ziyarar Blinken na biyo bayan taron shugabannin kasashen Africa da ya gudana a birnin Washington a watan Disamban 2022.

 

Yayin da yake jawabi a kasar Cape Verde, Blinken ya ce yanzu lokaci ne da duniya ke sha’awar mu’amala da Africa don haka ba za’a bar Amurka a baya ba, la’akari da muhimmancin da Afrika ke da shi da kuma tarin arziki.

 

Kusan dukannin kasashen yammacin Africa na fama da matsalolin tsaro da suke da alaka ta kai tsaye da kungiyoyin masu ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.