Isa ga babban shafi
Bahrain

An gudanar da zana'ida a Bahrain

Dubban mutane cikin fushi sun halarci zana’idar wadanda suka hallaka, yayin zanga zangar nuna kiyayya wa gwamnatin kasar Bahrain.Mutanen yayin sallar Jumma’a, bayan zana'idar, sun nemi kawo karshen masarautar kasar baki daya, tare da bayyana cewa kisan gilla gwamnati ta yiwa samu zanga zangar su hudu a jiya Alhamis.Rohotanni sun nuna cewa an samu masu zanga zangar nuna goyon baya wa gwamnatin kasar ta Bahrain dake tsaka mai wuya, kuma sun samu kariya daga jami’an tsaro, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AP (Associated Press) ya ruwaito. An kiste tankokin yaki a wasu mahimman wuraren Manama babban birnin kasar, domin tabbatar da dakile zanga zangar nuna adawa da gwamnatin kasar. Kuma ma’aikatar harkokin cikin gida ta bayyana cewa sojojin sun dauki duk matakan tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali.Kasar ta Bahrain ta na karkashin mulkin masarautar dake bin darikar Sunna, amma ‘yan Shiya mafiya rinjaye ke gudanar da zanga zangar ta adawa. 

Masu zanga zangar kasar Bahrain
Masu zanga zangar kasar Bahrain Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.