Isa ga babban shafi
Venezuela

An ware mako guda a Venezuela domin zaman makokin rasuwar Hugo Chavez

Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya mutu bayan kwashe watanni yana jinyar cutar Cancer. Lamurra a kasar Venezuela sun tsaya cak bayan mutuwar shugaban inda al’ummar kasar za su sake jefa kuri’ar zaben sabon shugaban kasa.

Al'ummar kasar Venezuela suna kuka domin rashin shugabansu Hugo Chávez
Al'ummar kasar Venezuela suna kuka domin rashin shugabansu Hugo Chávez REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

Mataimakin shugaban kasa Nicolas Maduro, wanda ya barke da kuka a lokacin da ya ke bayar da sanarwar mutuwar Shugaba Chavez, yace gwamnatin kasar ta girke jami’an tsaro domin kare lafiyar al’umma da wanzar da zaman lafiya a cikin kasar.

Gwamnatin kasar ta ware tsawon mako guda domin zaman makokin rasuwar Chavez.

Babban Ministan kasar yace nan da kwanaki 30 ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa.

Marigayi Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez
Marigayi Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez REUTERS/Jorge Silva/Files

Shugaba Hugo chavez mutum ne mai ra’ayin gurguzu wanda ke da kima ga mutanen Vanezuela saboda ci gaban da ya kawo wa kasar.

Wasu suna ganin, Hugo Chavez ya samu amintaka da daraja daga sauran shugabannin kasashen Latin Amurka saboda irin adawar da ya ke yi da Amuka.

Amma a bangaren ‘Yan adawa, Hugo chavez, Shugaba ne wanda ya gudanar da mulkin Danniya a Venezuela.

An haifi Hugo Rafeal Chavez a ranar 28 ga watan Julin shekarar 1954 a birnin Barinas wanda iyayensa malaman makaranta ne.

Chavez ya yi karatu mataki na farko a Barinas kafin ya shiga makarantar aikin soji a Caracas babban birnin Venezuela, inda ya kammala a 1975.

Chavez yana da ra’ayin, Sojoji na iya hambarar da gwamnatin farar hula idan aka samu gwazawa daga gwamnatin.

A shekarar 1992 Hugu Chavez yana cikin sojin da suka yi yunkurin hambarar da gwamnatin shugaba Perez saboda kaddamar da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.

Chavez ya kwashe shekaru biyu a gidan yari kafin ya sake kaddamar da jam’iyyarsa ta neman kafa jamhuriyya ta biyar a kasar.

A shekarar 1998 ne aka zabi Hugo Chavez a matsayin shugaban kasa wanda ya samu rinjayen kuri’u kashi 56.

A shekarar 2000 ne aka sake zaben Hugo Chavez wa’adi na biyu bayan sauya kundin tsarin mulkin kasar Venezuela wanda ya tsawaita wa’adin shugabanci daga shekaru 5 zuwa shida.

A shekarar 2002 ne ‘Yan kasuwa da attajirai suka gudanar da zanga-zanga domin adawa da mulkin Hugu Chavez, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19. A lokacin ne kuma ‘sojoji suka hambarar da Chavez tare da kargame shi gidan yari.

Bayan sa’oi 47 ne kuma dubban magoya bayan Chavez da sojoji da ke biyayya ga shugaban suka dawo da Chavez a kujerarsa.

A ranar 10 ga watan Junin shekarar 2011 Hugo Chavez ya fara zuwa kasar Cuba domin neman maganin cutar Cancer.

Chavez ya samu nasarar lashe zabe a 2012 amma saboda rashin lafiyar shugaban, gwamnatin shi ta fuskanci suka daga ‘Yan adawa kafin shugaban ya dawo gida daga kasar Cuba a ranar 18 ga watan Fabrairu domin ci gaba da jinya a wata asibitin Caracas.

Chavez ya mutu ne a ranar 5 ga watan Maris bayan rashin lafiyar shi ta tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.