Canada ta janye tallafin da ta ke ba Burkina Faso
Gwamnatin kasar Canada ta fitar da sanarwar janye tallafin taimako da ta ke ba kasar Burkina Faso saboda Sojoji sun kwace mulki bayan ‘Yan adawa sun tursasawa Blaise Compaore yin murabus. Ofishin Ministan kula da bayar da tallafi ga kasashen waje yace Canada ta janye tallafin da ta ke ba Burkian Faso saboda halin da kasar ke ciki a halin yanzu.
Wallafawa ranar:
Kasar Canada dai na daya daga cikin kasashen da ke ba kasar Burkina Faso tallafi gwajen bunkasa ayyukan noma da masana’antu da kiwon lafiya da kuma kare hakkin Mata.
Canada tace zata ci gaba da Burkian tallafi idan kasar ta dawo a turbar dimukuradiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu