Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinu

Benjamin Netanyahu ya lashe zaben kasar Isra’ila

Firaiministan kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya lashe zaben da aka gudanar a kasar, bayan da ya ka da bangaren ‘ya’yan jam’iyyun hamayya da gagarumin rinjaye

Le Premier ministre Benyamin Netanyahu salue ses partisans au quartier-général du Likoud, le 18 mars 2015.
Le Premier ministre Benyamin Netanyahu salue ses partisans au quartier-général du Likoud, le 18 mars 2015. REUTERS/Amir Cohen
Talla

A sakamakon farko na zaben kasar ta Isra’ila dai ya nuna yadda Firaiminista Benjamin Netanyahu ke kan gaba da akalla kashi 24 bisa 100.

Wannan dai ya nuna cewar jam’iyyar Likud Party ta Firaiministan ta sha gaban jam’iyyar adawa a zaben da zai rabe gardama kan makomar Palesdinu ga kasar ta Isra’ila, bisa alwashin da Firaiministan ya yi na cewar idan ya samu nasara, babu sauran batun kafa kasar Palesdinu.

Sakamakon dai ya nuna cewar daga cikin sama da kashi 70% na kuri’un da aka kirga a zaben, jam’iyyar Likud ta iraiministan ce ke kan gaba da akalla kashi 23% cikin 100% a yayin da Jam’iyyar Zionist union ke da kashi 19, kamar yadda Alkalumman da hukumar zaben kasar ta Isra’ila ta fitar a karon farko.

Wata kafar sadarwar Radio ta cikin gida a kasar ta Isra’ila, ta bayyana cewar sakamakon ya kumshi kujeru 30 da jam’iyyar mai mulki ta sama daga cikin 120 na Majlisar kasar, a yayin da Jam’iyyar Zionist ta samu 24.

Dama dai Firaiminista Netanyahu ya yi ikrarin samun nasara a zaben da ake ganin ka iya bashi damar ci gaba da mulki a wa’adi na 3, koda yake yana da matukar bukatar masu mara masa baya, domin ya samu majingina.

A lokacin gangamin yakin neman zabensa dai Firaiminista Netanyahu ya saka batun sha’anin tsaro ne a gaba, tare da yin alwashin kawar da batun kafa kasar palesdinu, a yayin da su kuma a nasu bangaren, shugabannin Palesdinawa ke matsa kaimi ga batun samar da ‘yantacciyar kasarsu.

Yanzu dai hankali ya karkata ga yadda Firaiminista Netanyahu zai iya dagula batun kafa kasar ta Palesdinu da tuni ta samu amincewar wasu daga cikin kasashen yammacin Duniya, ciki kuwa hadda Birtaniya da Faransa, kazalika da Majalisar dunkin Duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.