Isa ga babban shafi
Switzerland

Mutanen Switzerland sun fi samun farin ciki a duniya

Switzerland ce ta fi kowace kasa zama a cikin farin ciki a duniya, yayin da Iceland ke bi mata da Demnark da Norway da Canada, kamar yadda wani sakamakon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna.

Tutar kasar Switzerland
Tutar kasar Switzerland REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Wannan shi ne karo na uku da aka fara fitar da rahoton a shekara wanda ke nazari akan yadda farin cikin ‘yan kasa zai taimaka a sauya yadda ake tafiyar da gwamnatoci.

Kasashen Finland da Sweden da New Zealand da Austalia na cikin jerin kasashe 10 da mutanen kasar ke cikin farin ciki.

Jami’an da suka gudanar da binciken sun diba ma’aunin ci gaban kasa da girman cin hanci da rashawa da yanayin ci gaban bangaren lafiya da kuma ‘yancin da mutane suke da shi wajen gudanar da lamurransu na yau da kullum.

Amurka tana matsayi na 15 a jerin kasashen da suka fi farin ciki, inda kasar Birtaniya ke mataki na 21.

Jamus mai karfin tattalin arziki a Turai na mataki na 26 ne, yayin da Faransa ke mataki na 29.

Kasashen Afghanistan da Syria, da yaki ya daidaita, sun bi sawun wasu kasashen Afrika 8 Togo da Burundi da Benin da Rwanda da Burkina Faso da Cote d’Ivoire da Guinea da Chadi da suke matakin karshe a farin ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.