Paparoma ya koka da hare haren Nukiliyan Hiroshima da Nagasaki
Paparoma Francis yace har yanzu hare hare bama baman Nukiliyan da aka kai a biranen Hiroshima da Nagasaki na Japan, suna ci gaba da jefa fargaba da tayar da hankulan jama’a, shekaru 70 bayan faruwar lamarin.
Wallafawa ranar:
Paparoman, dake magana yau Lahadi, ranar da ake cika shekaru 70 da kai hare haren, ya nemi a haramta makaman Nukuliya, da ma sauran makaman kare dangi a fadin duniya.
Ranar 6 ga watan Augustan shekarar 1945, wani jirgin saman yakin Amurka ya jefa bom a birnin Hiroshima, ya kashe kimanin mutane dubui 140, lokacin da ake gab da kawo karshen yakin duniya na 2.
Kwanaki 3 bayan nan ranar 9 ga wata aka sake jefa wani makamin mai guba a birnin of Nagasaki, da shi kuma ya hallaka fiye da mutane dubu 70, rana 15 ga wata kuma Japan ya mika wuya a yakin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu