Isa ga babban shafi
Japan

Shekaru 70 da Amurka ta kai hari a Nagasaki

A yau lahadi al’ummar kasar Japan na juyayi dangane da cika shekaru 70 da Amurka ta yi amfani da bam na nukiliya kan al’ummar garin Nagasaki a lokacin yakin duniya na biyu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 74 a lokaci daya.

Garin Nagasaki bayan da Amurka ta harba makamin nukilya a kansa shekar 1945
Garin Nagasaki bayan da Amurka ta harba makamin nukilya a kansa shekar 1945 REUTERS/Shigeo Hayashi/Nagasaki Atomic Bomb Museum/
Talla

Firaministan kasar Shinzo Abe, tare da wakilai daga kasashen duniya 75 cikinsu har da jakadiyar Amurka a kasar Caroline Kennedy, suka halarci wani biki da aka shirya a safiyar yau lahadi domin tunawa da wannan rana.

A ranar alhamis da ta gabata ne dai aka gudanar da irin wannan juyayi a game da harin da Amurka ta kai wa kasar ta Japan a lokacin yakin duniyar ba biyu a garin Hiroshima, inda a can ma aka samu mutuwar dubban mutane.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.