Amurka-Syria
Amurka za ta karbi ‘yan gudun hijirar Syria dubu 10
Shugaban Amurka Barack Obama ya bayar da umurni kasar ta karbi ‘yan gudun hijirar Syria akalla dubu 10 amma sai a cikin shekara mai zuwa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Mai magana da yawun fadar shugaban na Amurka Josh Earnest ya ce za a karbi ‘yan gudun hijira 1500 a wannan shekara yayin da sauran dubu 10 za a ba su damar shiga Amurka a shekarar badi.
A kowace shekara dai Amurka na karbar baki daga kasashen da ke fama da rikici akalla dubu 70, to sai dai tana dari-darin karba ‘yan kasar ta Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu