Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka za ta kori 'Yan gudun hijira-Trump

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Republican, Donald Trump ya bayyana cewa, muddin ya lashe zabe, zai mayar da dubban ‘Yan gudun hijirar Syria kasarsu.

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iayyar Republican, Donald Trump.
Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iayyar Republican, Donald Trump. REUTERS/Gretchen Ertl
Talla

Trump ya shaidawa gidan Talabijin na CNN haka ne, a daidai lokacin da jiragen yakin Rasha suka fara lugudan wuta a Kasar Syria da zummar taimkawa wajan murkushe mayakan ISIS.

A cewar Trump, idan ya zama shugaban Kasar Amurka zai mayar da 'yan gudun hijirar Syria dubu 200 kuma ya ce ya kamata yan gudun hijrar da duniya su san da haka tun yanzu.

Kana ya ce, ba ta yadda zasu baiwa yan gudun hijra mafaka, inda wata kila a cikinsu akwai yan kungiyar ISIS dake da’awar jihadi.

Trump dai ya ce a yanzu ‘yan gudun hijirar zasu iya samun mafaka a Amurka saboda gwamantin Barack Obama da ya bayyana a matsayin mai rauni.

Amurka dai ta bayyana cewa ta na sa ran karban ‘yan gudun hijra dubu 100 nan da shekara ta 2017 kuma a cikin shekara mai zuwa ne za ta karbi  yan gudun hijra dubu 85,inda kusan dubu 70 daga cikinsu 'yan Kasar Syria ne  kamar John Kerry ya sanar sakataren harkokin wajen Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.