Isa ga babban shafi
Amurca

Dangantakar Amurka da kasar Cuba

Shugaba Obama zai kai wata ziyara kasar Cuba a ranar 21 ga watan Maris sanarwa daga Fadar gwamnatin Amurka ta white house .Amma sai dai fadar tace ba lallai ne shugaba Obama ya gana da tsohon shugaban kasar wato Fidel Castro ba. 

Tutocin Amurka da Cuba
Tutocin Amurka da Cuba © Reuters
Talla

Ziyarar dai na zuwa ne a wani lokaci da kasashen biyu ke kokarin kawo karshen zaman dar dar tsakaninsu .
Shugaba Obama shine shugaban Amurka mai ci na farko da ya ziyarci kasar tun shekarar 1928.
Gwamnatin Cuba dai na fassara ziyarar a matsayin wani mataki na karfafa hulda tsakanin su, da ta samo usuli tun watan yulin shekarar data gabata
Acewar shugaban na Amurka zai bijiro da batun hakkin bil adama a tattaunawar da shugaban Cuba.
To sai dai kuma a cewar fadar gwamnatin amurkan babu tabbacin za’a gana tsakanin shugaba Obama da tshohon shugaban kasar Fidel Castro.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.