Isa ga babban shafi
Brazil

Zanga-zangar neman Rousseff ta sauka daga mulkin Brazil

‘Yan adawa a kasar Brazil sun yi kira da a gudanar da zanga-zangar gamaa-gari domin tilastawa shugabar kasar Dilma Roussef sauka daga kan mukaminta.

Shugabar Brazil, Dilma Rousseff
Shugabar Brazil, Dilma Rousseff REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

‘Yan adawar na zargin Roussef ne da nuna gazawa a fagen yaki da rashawa, yayin da a daya bangare ake zargin mukarrabanta ciki har da tsohon shugaban kasa Lula De Silva da rashawa.

Cin hanci ko rashawa da ake yi wa gwamnatin Dilma, na daga cikin dalilan da suka jefa tattalin arzikin kasar a cikin mawuyacin hali a cewar masu adawa da ita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.