Isa ga babban shafi
Amurka

An soki matar Trump don kwaikwayar matar Obama

Uwargidan dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump ta sha caccaka kan jawabin da ta gabatar a babban taron kasa na jam’iyyar, inda ta kwaikwayi uwargidan shugaba Barack Obama.

Uwargidan Donald Trump, Melania Trump a taron Republican a Amurka
Uwargidan Donald Trump, Melania Trump a taron Republican a Amurka REUTERS/Mike Segar TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Masharhanta sun ce, Melania Trump ta gabatar da jawabin da ya yi kama da irin wanda Michelle Obama ta gabatar a shekara ta 2008 a irin wannan taron.

A jawabinta, Melinia ta ce “ Iyayena sun koyar da ni dabi’ar kwazo domin samun abinda mutun ke nema a rayuwa”

Sannan sun ce mata “Kalaman mutun sune kimarsa, kuma ya aiwartar da abinda ya fadi tare da cika alkawarin da ya dauka, kana ya girmama mutane”

Wadannan kalaman sun yi kama da na Michelle inda ta ce, “Ni da Barack mun taso cikin tsarin tarbiya guda, inda aka nuna mana cewa, mutun na bukatar kwazo domin samun abinda ya ke nema a rayuwa kuma kalamansa ne kimarsa, kana ya aikata abinda ya ce zai yi, sannan ya girmama mutane ko da bai san su ba ko kuma bai gamsu da su ba”

Matar Trump ta ci gaba da cewa, “ Iyayena sun koya min yadda zan nuna dabi’ar a rayuwata kuma wannan ne darasin da zan koyar da danmu, kana akwai bukatar mu koyar da darasin ga daukacin ‘ya’yan al’umomi masu zuwa saboda muna son 'ya'yanmu su san cewa, iya kokarinka iya tikewarka wajen cimma burinka”

Ita kuwa Mrs. Obama cewa ta yi a wancan lokacin “Ni da Barack Obama mun yi shirin inganta rayuwarmu a kan wannan tsarin tarbiyar, sannan kuma mu koyar da ita ga sauran al’ummomi masu zuwa saboda muna son ‘ya’yanmu da sauran 'ya'yan daukacin jama’ar kasar nan su san cewa, iya kokarinka iya tikewarka wajen cimma burinka”

A karon farko kenan da Mrs.Trump ta gabatar da jawabi tun lokacin da aka fara yakin nneman zaben shugabancin Amurka kuma kwararrun marubuta ne suka taimaka mata wajen rubuta jawabin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.