Isa ga babban shafi
Jamus

Faransa da Jamus za su kawar da rikice-rikice

Shugaban Faransa, Francois Hollande da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel sun amince su kara hada kai don kawar da tashe-tashen hankulan da ke cika wa da jama’a.

Jami'an tsaron Jamus a kusa da shagon Olympia, inda dan bindigar ya kashe mutane 9 a ranar Jumma'a
Jami'an tsaron Jamus a kusa da shagon Olympia, inda dan bindigar ya kashe mutane 9 a ranar Jumma'a
Talla

Wannan na zuwa ne bayan harin da wani Bajamushe dan asalin kasar Iran ya kai katafaren shagon Olympia da ke birnin Munich inda ya hallaka mutane 9.

Shugabannin kasashen duniya daga Arewacin Amurka da Turai da kuma kasashen Musulmi duk sun yi Allah- wadai da harin na ranar jumma’a.

Har yanzu dai ana ci gaba da bincike don gano dalilin da ya tinzira matashin mai suna David Ali Sonboly kaddamar da harin, duk da cewa ana tunanin farmakin na da nasaba da kisan kare dangin da wani dan bindiga mai suna Anders Behring Brevivik ya yi a Norway, shekaru biyar da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.