Isa ga babban shafi
Jamus

Dan bindigar Munich ba ya da alaka da IS

‘Yan sanda a kasar Jamus sun ce dan bindigar da ya harbe mutane 9 ya damu ne da yin harbi kamar dan bindigar Norway Ander Breivik wanda ya kashe mutane 77 a 2011.

Shagunan Olympia  Munich inda dan bindiga ya kashe mutane 9 a Jamus
Shagunan Olympia Munich inda dan bindiga ya kashe mutane 9 a Jamus REUTERS
Talla

Dan bindigar wanda Bajamushe ne kuma dan asalin Iran an bayyana sunan shi a matsayin David Ali Sonboly wanda ya bude wa mutane wuta a wani gidan abinci inda shaguna suke da yawa a Munich.

‘Yan sandan Jamus sun ce dan bindigar ba ya da alaka da kungiyar IS da ke da’awar jihadi, wanda ake hasashen ya kashe kansa bayan musayar wuta da ‘Yan sanda.

Amma binciken ‘Yan sandan ya gano dan bindigar yana da tabin hankali.

Wadanda dai ya kashe ‘yan kasashen waje ne da suka hada da ‘Yan Turkiya 3 da ‘Yan Kosovo 3 da kuma Dan Girka guda.

A jawabinta na farko bayan kai harin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce birnin Munich ya fada cikin fargaba da tsoro.

Wannan harin dai ya kara razana Turai musamman bayan hare haren Faransa da Belgium.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.