Isa ga babban shafi
G20

Ficewar Birtaniya barazana ce ga duniya- G20

Kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki da aka fi sani G20 tayi gargadin cewa, ficewar kasar Birtaniya daga tarayyar turai barazana ce ga tattalinarzikin duniya.

Kasashen G20 sun bayyana fargaba kan irin illar da ficewar Birtaniya za ta yi wa tattalin arziki duniya
Kasashen G20 sun bayyana fargaba kan irin illar da ficewar Birtaniya za ta yi wa tattalin arziki duniya
Talla

Kungiyar ta G20 ta sanar da haka ne a jiya a wurin taron Ministocin kudi da kuma shugabannin bankunan kasashe a birnin Chengdu na kasar China.

Duk da bayyana fargabar yiwuwar samun koma bayan tattalin arziki a duniya saboda ficewar Birtaniya da ga EU, Ministocin sun jaddada cewa suna da karfin shawo kan wannan matsalar, sannan kuma za su kyautata dangantakarsu da Birtaniyar.

Kazalika sanarwar bayan taron ta ce, tashe-tashen hankula a sassan duniya da hare haren ta’addanci da kuma kwararar 'yan gudun hijira zuwa nahiyar turai na daga cikin abubuwan da ke haifar da kalubale ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Sai dai kuma Ministocin sun bayyana ficewar Birtaniya daga tarayyar Turai a matsayin kalubale mafi girma.

Baya ga haka kasashen na G20 sun ce, jan kafa wajen tattaunawa tsakanin Birtaniya da EU game da matakan ficewarta na barazanar dada sabbaba shigar tattalin arzikin sauran kasashen duniya cikin wani hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.