Isa ga babban shafi
Syria- Rasha

Jiragen yakin Rasha sun kashe IS 30 a Raqa

Jiragen yaki na kasar Rasha sun kai wani kazamin farmaki sansanonin ‘yan kungiyar IS dake Raqa a Arewacin kasar Syria inda aka kashe mutane akalla 30. 

Rukunin wasu gine-gine da aka lalata a yakin Syria
Rukunin wasu gine-gine da aka lalata a yakin Syria REUTERS/Khalil Ashawi
Talla

Masu sanya idanu kan yakin Syria sun gaskata cewa akwai wasu mutanen akalla 70 da suka jikkata.

Babu bayanai na wadan da aka gaskata ‘yan kungiyar IS ce, da kuma wadanda ba ‘yan kungiyar ce ba.

Hukumomin Rasha sun bayyana cewa wasu jiragen sama na yaki samfurin Tupolev suka kai samamen a yankin Raqa, inda suka lalata wata masana’antar harhada makamai masu guba da sansanin horas da mayakan kungiyar ta IS.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.