Isa ga babban shafi
Canjin Yanayi

Yarjejeniyar Paris za ta fara aiki cikin kwanaki 30

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yarjejeniyar birnin Paris kan dumamar yanayi za ta fara aiki a cikin kwanaki 30 masu zuwa, saboda a cewar Majalisar, an samu adadin kasashen da ake bukata da suka rattabawa yarjejeniyar hannu.

An cimma yarjejeniyar don rage yawan hayaki mai gurtaba muhalli a duniya
An cimma yarjejeniyar don rage yawan hayaki mai gurtaba muhalli a duniya REUTERS/Kim Kyung-Hoon/
Talla

Sanarwar da hukumar kula da batun na sauyin yanayi da ke karkashin Majalisar ta Dinkin Duniya ta fitar ta bayyana cewa, kawo yanzu an samu adadin kasashe 72 wadanda ke fitar da fiye da kashi 52 cikin 100 na gaz da ke gurbata yanayin da suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar.

Saboda haka ne hukumar ta UNFCCC ke cewa a yanzu dai, an samu adadin kasashen da ake bukata, illa kawai fara aiki da yarjejeniyar wadda ake ganin cewa ba karamar nasara ba ce ga kokarin da ake yi na rage yawan tururi da ke gurbata yanayin.

Tuni dai kasashen Amurka da China da kuma Indiya da ke sahun gaba sakamakon yawan masana’antun da suke da su suka amince da yarjejeniyar, yayin da a wannan mako majalisar dokokin tarayyar Turai ta amince da hakan.

Ana dai fatan fara aiki da yarjejeniyar ne kafin taron kasashen duniya kan dumamar yanayi da zai gudana daga ranar 7 zuwa 18 ga watan Nuwamba mai zuwa a kasar Maroko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.