Isa ga babban shafi
Amurka-Faransa

Dole ne Amurka ta yi aiki da yarjejeniyar Paris

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya bayyana cewa, wajibi ne kasar Amurka ta mutunta yarjejeniyar dumamar yanayi da aka cimma a lokacin shugabancin Barack Obama. Wannan na zuwa ne bayan nasarar da Donald Trump ya samu a zaben Amurka, abin da ake ganin zai haifar da barazana ga makomar yarjejeniyar.

Shugaban Faransa, Francois Hollande tare da wasu shugabannin duniya da suka halarci taron sauyin yanayi a birnin Marrakesh na Morocco
Shugaban Faransa, Francois Hollande tare da wasu shugabannin duniya da suka halarci taron sauyin yanayi a birnin Marrakesh na Morocco Fadel Senna/AFP
Talla

Shugaba Hollande ya ce, ya zama wajibi ga Amurka da ta kasance mafi karfin tattalin arziki a duniya, ta mutunta alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar da zimmar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli a duniya.

Hollande da ke magana a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya da ake gudanarwa kan sauyin yanayi a birnin Marakesh na Morocco ya ce, mutunta wannan yarjejeniyar, zai amfani Amurka kamar yadda zai amfani sauran al’ummar duniya.

A baya dai, zababben shugaban na Amurka, Doanld Trump mai jiran gado, ya bayyana  yarjejeniyar a matsayin shiririta wadda ya ce, kasar China ce ta yi sanadiyar ta.

Mr. Trump ya yi barazanar warware yarjejniyar wadda aka cimma da nufin kare lafiyar al’umma daga fuskantar bala’oi da suka hada da fari da ambaliyar ruwa da kuma matsanancin yanayin zafi.

A bangare guda, sakataare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ya yi fatan Amurka za ta yi aiki da yarjejeniyar a karkashin mulkin Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.