Isa ga babban shafi
Amurka

A na ci gaba da kira zuwa ga Trump kan dumamar yanayi

Kasashen Duniya, Manyan ‘Yan kasuwa da manyan Jami’an diflomasiyar Amurka sun bukaci Zababben shugaban kasar Donald Trump da ya mutunta yarjejeniyar magance matsalar dumamar yanayin da aka kulla a Paris.

Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump
Zababben Shugaban kasar Amurka Donald Trump 路透社照片
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bayyana tashin hankalin da zai addabi duniya muddin shugabanni suka kasa daukar matakin magance matsalar da ke haifar da dumamar yanayi a taron da ake yi a kasar Morocco.

A wata budaddaiyar wasika da kamfanoni da masu zuba jari 360 suka rubutawa Donald Trump sun bukace shi da ya aiwatar da yarjejeniyar ta Paris.

A lokacin yakin Neman zaben Shi, Donald Trump ya bayyana adawar sa da yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma a birnin Paris kan rage adaddin gurbattaciyar iska da suke fitarwa don magance matsalolin dumamar yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.