Isa ga babban shafi
ICC-Congo

ICC ta tsawaita zaman Bemba a gidan kaso

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta kara wa’adin shekara guda kan hukuncin zama a gidan yari na shekaru 18 da ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban Jamhuriyar Demokradiyar Congo Jean-Pierre Bemba.

Jean-Pierre Bemba
Jean-Pierre Bemba REUTERS/Michael Kooren
Talla

Kotun ta kara wa Bemba wa’adin ne bayan ta same shi da laifin bada cin hanci ga wasu shaidu a shari’arsa da kotun ta ICCn ke saurara bisa aikata laifukan yaki a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a shekarun 2002 da 2003.

Kotun ta kuma umarci Bemba da ya biya tarar kudi Euro dubu 300 da za a bai wa wadanda mayakansa suka ci zarafi a Afrika ta Tsakiya.

Kotun ta bai wa Bemba umarnin sanya kudin tarar a cikin asusunta nan da watanni uku don tallafa wa mutanen da aka ci zarafin nasu da kuma gyara wuraren da aka lalata a lokacin rikicin.

A yayin yanke hukuncin, mai sharia Bertram Schmitt ya ce, akwai bukatar daukan irin wannan matakin don tsawatarwa musamman ga wadanda ke shirin aikata irin laifin Bemba nan gaba.

Har ila yau, kotun ta yanke wa makusantan Bemba hudu hukuncin daurin watanni shida zuwa biyu da rabi saboda samun su da hannu wajen taimaka ma sa aikata laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.