Isa ga babban shafi
Amnesty

An samu sassaucin hukuncin kisa a duniya- Amnesty

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta ce, adadin mutanen da aka kashe ta hanyar zartas ma su da hukuncin kisa a sassan duniya ya ragu a shekarar 2016 da akalla kashi 37 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekara ta 2015.

Amnesty ta ce an samu raguwar kisan mutane a sassan duniya a bara
Amnesty ta ce an samu raguwar kisan mutane a sassan duniya a bara REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

A rahoton da ta fitar a wannan Talata, kungiyar ta bada da misali da kasar Iran, in da aka samu raguwar kisan da kashi 42 cikin 100, sai kuma Pakistan da aka samu raguwar kashi 73.

Sai dai rahoton ya nuna alkaluman mutanen da aka kashe a bara a China sun zarce dukkanin alkaluman da aka tattara a sauran kasashen duniya.

Amnesty ta ce, an fi yanke wa manoma mara sa galihu hukuncin kisa a China, yayin da gwamnatin shugaba Xi Jinping ke sassauta hukuncin kisan kan manyan mutane masu hannu da shuni.

Wani rahoto da gidauniyar Dui Hua mai cibiya a Amurka ta fitar, ya ce, kimanin mutane dubu 2 aka kashe a China a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.