Trump na nazarin daukan matakin soji kan Venezuela
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, yana duba yiwuwar daukan matakin soji a matsayin martani game da rikicin Venezuela da ya ki ci ya ki cinyewa.
Wallafawa ranar:
Sai dai tuni, gwamnatin Venezuela ta gaggauta yin watsi da yunkurin Trump da ta bayyana a matsayin hauka.
Amurka ta kakaba takunkumai kan shugaba Nicolas Maduro da wasu aminansa sakamakon matakin da ya ke dauka na murkushe ‘yan adawar Venezuela .
Kimaniun watanni hudu kenan da ake fama da rikicin siyasa a Venezuela , in da kusan mutane 130 suka rasa rayukansu sakamakon tarzoma tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar adawa da gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu