Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta sake harba makami mai linzami

Korea ta Arewa ta yi sabon gwajin makami mai linzami da ya ratsa ta sararin samaniyar Japan, abin da ya haifar da sabuwar fargabar tashin hankali a yankin.

Korea ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami a wannan Jumma'ar
Korea ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami a wannan Jumma'ar STR / KCNA VIA KNS / AFP
Talla

Wannan an zuwa ne bayan Korea ta yi barazanar nitsar da Japan a karkahsin kasa da kuma mayar da Amurka toka da makaminta na nukiliya saboda goyan bayan sabbin takunkuman da aka kakaba ma ta.

Kwanaki biyu kenan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wasu jerin takunkuman da Amurka ta gabatar domin ladabtar da Korea.

Korea ta Arewar ta kuma bukaci rusa Kwamitin Sulhu wanda ta ce, ya zama wani dandalin bai wa kasashe cin hancin kudi domin goyan bayan kudirorin Amurka.

Korea ta ce, da wannan mataki na Majalisar Dinkin Duniya, babu dalilin ci gaba da wanzuwar kasar Japan kusa da ita.

Firaministan Japan, Shinzo Abe ya bayyana cewa, kasarsa ba za ta amince da wannan takalar mai matukar hatsari daga Korea ta Arewa ba.

Wani lokaci a yau ne Kwamitin Sulhun zai sake wani zama don tattaunawa kan sabon gwajin makamin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.