Isa ga babban shafi
Amurka

Amurkawa na zanga-zanga kan dokar mallakar bindiga

Dubban amurkawa ne yau ke shirin sake gudanar da wata zanga-zangar adawa da matakin gwamnati na samar da gyare-gyare a dokar mallakar bindiga, tun bayan kisan wasu mutane 17 a wata makaranta da ke birnin Florida cikin watan jiya.

A watan da ya gabata ne dai wani matashi ya harbe dalibai 17 har lahira da bindigarsa, matakin da ya haddasa kiraey-kirayen samar da gyare-gyare a dokar mallakar bindigar.
A watan da ya gabata ne dai wani matashi ya harbe dalibai 17 har lahira da bindigarsa, matakin da ya haddasa kiraey-kirayen samar da gyare-gyare a dokar mallakar bindigar. REUTERS/Corinna Kern
Talla

A jiya juma’a ne gwamnatin Amurka ta sanar da cewa akwai yiwuwar aiwatar da wasu gyare-gyare a dokar mallakar bindigar dama cinikayyar makamai ko da ya ke dai masu fafutukar kare hakkin dan adam a kasar na ganin akwai bukatar bai wa majalisa damar kada kuri’a kan batun.

Wasu dai na kallon matakin a matsayin yunkurin hanawa al’umma sakat baya ga rage musu ikon kare kansu a lokacin rikici.

A bangare guda kuma wasu Amurkawan na fafutukar ganin an aiwatar da gyaren don samar da sauki ga yawan kashe-kashen bag aira-babu-dalili da ke yawan faruwa a kasar.

Batun mallakar bindigar dai yanzu haka ya haddasa rarrabuwar kai a kasar, inda wasu ke ganin akwai bukatar haramta mallakar bindigar yayinda wasu ke kallon matakin a matsayin yunkurin tauye hakkin bil’adama.

Sashe na biyu na kundin tsarin mulkin Amurka dai ya amince da mallakar bindigar ga kowanne dan kasa don kare kansa haka zalika hukumar kula da makamai ta kasar NRA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.