Isa ga babban shafi
Duniya

Mai yiwuwa ba za a taba nasarar kawar da coronavirus daga doron kasa ba - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tace mai yiwuwa ba za a taba samun nasarar kawar da annobar coronavirus ko COVID-19 daga doron kasa ba, dan haka ya zama dole al’ummar duniya ta koyi yadda za ta rayu da cutar.

Darakatan shirye-shiryen ayyukan gaggawa na hukumar WHO Michael Ryan, tare da Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar ta WHO a birnin Geneva. 9 ga Maris, 2020. March 9, 2020.
Darakatan shirye-shiryen ayyukan gaggawa na hukumar WHO Michael Ryan, tare da Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar ta WHO a birnin Geneva. 9 ga Maris, 2020. March 9, 2020. AFP
Talla

Darakatan ayyukan gaggawa na hukumar ta WHO Michael Ryan yace duniya na cikin tsaka mai wuya ne, la’akari da cewar, har yanzu babu wanda yake da hasashe, ko tabbacin ranar da sabuwar cutar da tayiwa duniya kawanya za ta zo karshe.

Yayin jawabi a birnin Geneva, Ryan yace coronavirus ka iya shiga cikin jerin cutukan da suka addabi duniya ba kuma tare da an yi nasarar kawar da su ba, irinsu HIV, da Tarin Fuka, wadanda a yanzu mutane suka fahimici yadda za su rayu dasu gami da samun kariya daga garesu bisa shawarwarin kwararru a fannin lafiya.

Hasashen Hukumar Lafiyar ta Duniya na zuwa ne a daidai lokacinda kasashe da dama ke daukar matakan sassauta dokar hana zirga-zirga da suka shafe makwanni da kafawa domin dakile yaduwar annobar ta coronavirus, wadda ta karya tattalin arziki kasashe, bayan tilastawa akalla rabin al’ummar duniya zaman gidan dole.

A watan disambar shekarar bara annobar coronavirus ko COVID-19 ta bulla a birnin Wuhan na kasar China, wadda zuwa lokacin wallafa wannan labara ta kama sama da mutane miliyan 4 da dubu 200, daga cikinsu kuma ta halaka kusan mutane dubu 300 a kasashe kusan 200 da ta kutsa cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.