Isa ga babban shafi
Facebook

Facebook ya nemi afuwar masu bibiyarsa bayan katsewar sa'o'i 7

Kamfanin Facebook, wanda ya mallaki shafukan sada zumunta na Whatsapp, Messenger da kuma Instgram, ya nemi afuwar masu bibiyar sa, bayan da ya samu wata gagaruwar tangarda wadda ta yi sanadiyyar katsewarsu har tsawon sa’o'i 7 a duk fadin duniya.

Tambarin kamfanin sada zumunta na Facebook da ke da mallakin Watsapp da Messenger.
Tambarin kamfanin sada zumunta na Facebook da ke da mallakin Watsapp da Messenger. REUTERS - Dado Ruvic
Talla

Sanarwar da kamfanin ya fitar a cikin daren ya gabata, ta ce an samu wannan matsala ce sakamakon wasu aikace-aikace da ya yi akan na’urorinsa, matsalar da ke zuwa a dai dai lokacin da majalisar dokokin Amurka ke shirin binciken kamfanin bisa zargin yi wa dimokuradiyya karen tsaye.

Wasu bayanai sun ce kamfanin na Facebook baya daukar matakan da suka dace, duk da masaniyar da ya ke da ita game da yada labaran karyar da ake yi da shi baya ga baiwa kananan yara damar cin karensu babu babbaka ba tare da daukar mataki ba.

Tun bayan katsewar shafukan na Facebook, Watsapp da kuma Instagram bayanai sun ce miliyoyin jama'a sun tsinci kansu a hali na kaduwa inda na’urar bibiya ta tsaro ta nuna yadda matsalar ta fi shafar al'ummomin da ke amfani da kafofin a yankuna irinsu birnin Washinton na Amurka da kuma Paris na Faransa.

Mai Magana da yawun kamfanin Facebook, wato Andy Stone da ke mika sakon neman afuwar kamfanin ga miliyoyin masu bibiyarsa cikin wani sako da ya wallafa ya ce sun yi kokarin aiki tukuru wajen magance matsalar a kankanin lokaci.

Wannan katsewar na zuwa ne kwana guda bayan wata mai tseguntawa ta ziyarci wani gidan talabijin na Amurka don bayyana yadda ta bankado wasu takardu ga hukumomi da ke zargin kamfanin ya san cewa yana rura matsalar nuna tsana da kuma shafar lafiyar kwakwalwar kanana yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.