Isa ga babban shafi
Haiti - Tsaro

Wadanda suka sace Amurkawa a Haiti sun bukaci dala miliyan 17

Masu garkuwa da mutane a kasar Haiti da suka kama wasu masu aikin bushara daga Amurka da Canada 17, cikin su harda kananan yara guda 5, sun bukaci a biya su diyyar Dala miliyan guda akan kowanne mutum guda da suka kama.

Motar 'yan sanda a Port-au-Prince baban birnin Haiti. 18/10/21.
Motar 'yan sanda a Port-au-Prince baban birnin Haiti. 18/10/21. Richard PIERRIN AFP
Talla

Garkuwa da mutanen da wata kungiyar Yan bindiga ta yi a Haitin ya dada fito da matsalolin tsaron da suka addabi kasar bayan kisan gillar da aka yiwa shugaba Jovenel Moise a watan Yuli.

Wata kungiyar da ake kira ‘Mawozo 400‘ wadda ta kwashe makwanni tana iko da yankin da aka sace masu aikin busharar tare da iyalan su, ta bukaci a biya ta Dala miliyan 17 a matsayin diyya kafin sakin mutanen 17.

Ministan shari’ar Haiti Liszt Quitel ya tabbatar da kungiyar ce ke rike da mutanen 16 da dan kasar Canada guda.

Quitel ya shaidawa Jaridar Washington Post cewar masu garkuwa da mutanen kan bukaci a biya su makudan kudade, amma daga bisani akan samu ragi idan an tattauna da su.

Masu busharar na aiki ne da wata kungiyar agaji ta Christain Aid dake da cibiya a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.