Isa ga babban shafi
Haiti

Masu garkuwa a Haiti sun nemi dala miliyan 17 kafin sakin 'yan mishan

Masu garkuwa da mutane a kasar Haiti dake tsare da wasu ‘yan mishan 17, cikinsu har da yara 5 da suka hada da Amurkawa da kuma ‘yan kasar Canada, sun nemi a basu dala miliyan 17 a matsayin kudin fansar mutanen da suka sace.

Wani sashi na yankin gabashin Port-au-Prince babban birnin kasar Haiti.
Wani sashi na yankin gabashin Port-au-Prince babban birnin kasar Haiti. Richard PIERRIN AFP
Talla

Satar mutanen ta baya bayan nan da daya daga cikin gungun masu aikata miyagun laifuka a kasar ta Haiti suka yi, ya bayyana karuwar matsalolin da kasar ke ciki a yanzu haka, tun bayan bayan kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban kasar Jovenel Moise a watan Yuli.

Wata kungiya da aka fi sani da ‘400 Mawozo, wadda ta shafe watanni tana iko da yankin da aka sace ‘yan Mishan din 17 ne ta bukaci a biyanta dala miliyan 17, kamar yadda wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ministan shari'ar Haiti Liszt Quitel ya shaidawa jaridar The Washington Post cewa, yawancin masu garkuwa da mutane suna neman makudan kudaden da ake ragewa yayin tattaunawar neman sakin wadanda suka sace, yana mai cewa har yanzu jami'an sa ba su shiga cikin tattaunawar ba.

'Yan mishan din da aka sace a Haiti dai na aiki ne a karkashin ma'aikatun Christian Aid na Amurka, wadanda aka sace a gabashin birnin Port-au-Prince yayin da suke kan hanyar komawa gida daga ziyartar gidan marayu da ke tsakanin babban birnin kasar ta Haiti dake kan iyaka da Jamhuriyar Dominican.

A watan Afrilu, mutane 10 ciki har da malaman Faransa guda biyu kungiyar 400 Mowozo ta sace, tare da tsare su tsawon kwanaki 20 a dai yankin dake gabashin birnin Port-au-Prince.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.