Isa ga babban shafi
TARON G20

Shugabannin kasashen G20 na babban taronsu a Roma na Italiya

Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 zasu bude babban taronsu wannan Asabar a birnin Roma na kasar Italiya, inda ake saran batun sauyin yanayi da batun sake farfado da tattalin arzikin duniya za su fi daukar hankali a taron wanda shine na farko da aka ganawa tun bayan barkewar annobar korona.

Franministan Italiya Mario Draghi da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres a Roma yayin taron G20, 29/10/21.
Franministan Italiya Mario Draghi da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres a Roma yayin taron G20, 29/10/21. AFP - ALBERTO PIZZOLI
Talla

Ganawar na kwanaki biyu da za a yi a birnin Rome, zakarun gwajin dafi ne kan shawo kan matsalar dumamar yanayi ta za’a tattauna a babban taron COP26 da zai fara a birnin Glasgow ranar litinin.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya gargadi shugabannin na G20 da su kara azama wajen daukar matakai" da kuma shawo kan rashin amincewa da juna domin cimma muradun yanayi.

An tsaurara matakan tsaro a birnin Rome yayin da shugaban Amurka Joe Biden ya isa babban birnin kasar Italiya, wanda yake kokarin an sauya babin Donald Trump na janye Amurka daga cikin yarjejeniyar yanayi.

China da Rasha

Shugaban Rasha Vladimir Putin da Xi Jinping na China, basuyi tattaki zuwa Rome ba, inda ake saran su halarci taron na fasahar hoton bidiyo.

Babban mai masaukin baki Mario Draghi, firaministan Italiya, ya yi kira da a dauki matakin "G20 kan bukatar takaita hauhawar yanayin zafi zuwa digiri 1.5" sama da matakin masana'antu, wanda shi ne manufa mafi girma da aka zayyana a cikin yarjejeniyar Paris ta 2015 kan sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.