Isa ga babban shafi
VATICAN

Easter: Fafaroma ya yi kira da akawo karshen yakin Ukraine

Shugaban mabiyar tarikar Katolika ta duniya Fafaroma Francis yayi kira da a kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar Ukraine. 

Shugaban mabiyar tarikar Katolika ta duniya Fafaroma Francis
Shugaban mabiyar tarikar Katolika ta duniya Fafaroma Francis AP - Alessandra Tarantino
Talla

Yayin gabatar da gabatar da sakon Easter da ke zuwa cikin rikicin Ukraine a dandalin Saint Peter da ke fadar Vatican, Ya ce akwai bukatar shugabannin kasashe su ji koken mutane na neman zaman lafiya.

Francis ya ce rikicin ya shafi ‘yan kasar Ukraine da dama inda miliyoyi suka zama ‘yan gudun hijira.

Rikicin Isra'ila da Falasdinwa

Har wayau, Fafaroma Francis ya kuma yi kira da a baiwa kowa damar shiga wuraren Ibada masu tsarki a birnin Kudus.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula tsakanin Isra'ila da Falasdinawa a birnin na Kudus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.