Isa ga babban shafi

Hukumar WTO ta yi gargadin fuskantar mashassaharar tattalin arziki a Duniya

Hukumar kasuwanci ta Duniya WTO ta yi gargadin cewa duniya na tunkarar wani yanayin kamfar tattalin arziki sakamakon rikice-rikice da dama, wanda ken una bukatar da ake da ita samar da sabbin tsare-tsare da zasu habaka tattalin arziki.

Darakta Janar ta hukumar kasuwanci ta Duniya Ngozi Okonjo-Iweala.
Darakta Janar ta hukumar kasuwanci ta Duniya Ngozi Okonjo-Iweala. AP - SALVATORE DI NOLFI
Talla

Darakta Janar ta WTO Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana cewa batutuwa masu alaka da yakin Rasha da Ukraine da kuma dumamar yanayi sun yi taron dangi wajen assasa tsadar kayaki musamman na abinci baya ga haddasa karancin makamashi a sassan duniya, dai dai lokacin da ake shirin fita daga matsalar da annobar cutar corona ta jefa duniya.

A jawabinta gaban taron kasuwanci da zuba jari na shekara-shekara da ke gudana a Geneva, shugabar ta WTO ta ce wajibi ne a samar da sabbin dabarun habaka tattalin arziki da za su ragewa duniya radadin halin da ake ciki da kuma barazanar da ke tunkarowa.

A cewarta ana cikin wani yanayi da kiri-kiri ake iya hango barazanar da tattalin arziki ke tunkara a don haka dole ayi aiki tukuru wajen laluben hanyoyin murmurewa tun gabanin fadawa a matsalar baki daya, ta yadda za a dauka matakan rage tasirin da illar ta mashassharar tattalin arziki za ta yiwa Duniya.

Ngozi Okonjo-Iweala ta kafa hujja da yadda dukkanin hasashen tattalin arzikin da Bankin Duniya da kuma asusun bada lamuni na Duniya suka yi ke nuna mummunar koma bayan da ke tunkaro Duniya.

Darakta janar ta WTO ta ce kasashe a yanzu na fama da matsalolin rashin tsaro, dumamar yanayi, tsadar kayan abinci da kuma tsadar makamashi dukkaninsu a lokaci guda, wanda kai tsaye zai iya ruguza kasashe da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.