Isa ga babban shafi

Abu ne mai wuya a iya cimma muradin kawar da talauci- Bankin Duniya

Bankin Duniya ya yi gargadin cewa, zai yi wahala a iya cimma muradin kawar wa ko kuma rage kaifin kangin talauci a duniya nan da shekarar 2030.

Kasashen Afrika ne sahun gaba a wadanda talauci ke wahalarwa a sassan Duniya.
Kasashen Afrika ne sahun gaba a wadanda talauci ke wahalarwa a sassan Duniya. AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Bankin ya kuma bayyana annobar corona da ta barke a matsayin babban dalilin da ya haifar da koma baya kan yakin da hukumomin kasa da kasa ke yi da talauci, cutar da ya ce ta ruguzu ci gaba da aka samu na tsawon gomman shekaru.

Rahoton ya ce talauci ya karu matuka yayin fama da annobar corona, inda akai hasashen cewar kimanin mutane miliyan 70 suka fada cikin tsananin talaucin a shekarar 2020 kadai, lamari mafi muni da duniya ta gani, tun bayan da aka fara bin diddigi halin da marasa karfi ke ciki daga shekarar 1990.

A bana kuwa mutane miliyan 95 kwararru suka yi gargadin cewa za su iya fadawa cikin kangin talauci nan da karshen shekara, sakamakon halin da tattalin arzikin duniya ya tsinci kansa a ciki.

Baya ga annobar corona, matsaloli masu alaka da dumamar yanayi na taka muhimmiyar rawa wajen mayar da hannun agogo baya a kokarin yaki da talauci, yayinda yakin Rasha da Ukraine a baya-bayan nan ya haddasa tsananin matsin rayuwa ga al'umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.