Isa ga babban shafi

Adadin yawan al'ummar Duniya ya cika biliyan 8- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, adadin yawan al’ummar da ke ban kasa a yanzu ya kai biliyan 8 bayan tarin jariran da aka haifa yau talata, sabanin biliyan 7 da ake dasu shekaru 12 da suka gabata.

Nahiyar Asiya ce kan gaba a samun tagomashin yawan jama'a.
Nahiyar Asiya ce kan gaba a samun tagomashin yawan jama'a. AFP - ARUN SANKAR
Talla

Sanarwar Majalisar da ke bayyana wannan alkaluma ta ruwaito Antonio Guterres na cewa matakin abin farin ciki ne said ai babban nauyi ne da ya sake rataya kan mahukunta dangane batutuwan da suka shafi jinkai da zaman lafiyar Duniya baya ga samar abubuwan more rayuwa.

A cewar Majalisar wannan adadi na nufin cewa al’ummar duniya sun karu da biliyan guda a cikin shekaru 12 da suka wuce.

Majalisar ta danganta wannan bunkasa ta al’ummar duniya da yadda ake samun tsawon rai, sakamakon irin ci gaba da aka samu a bangaren kiwon lafiya, sarrafa abinci mai gina jiki da kuma dabarun kiyaye tsaftar jiki da ta muhalli.

A kasashe matsakaita a fannin tattalin arziki, akasari a nahiyar Asia ne aka fi samun yawan jama’a a cikin shekaru 10 da suka wuce, inda yawansu ya karu da miliyan dari 7 tun daga shekarar 2011.

Amma a yayin da da dama suke nuna damuwar cewa mutane biliyan 8 sun yi wa duniya yawa, akasarin kwararru na cewa babbar matsalar ita ce  yadda masu hannu da shuni suka yi kane kane a kan arzikin duniya.

Sai dai duk a yayin da al’ummar duniya suka kai wannan adadi, kwararru sun ce ya yi ta raguwa da kasa da kaso 1 a duk shekara, abin da suke ganin shi zai hana yawan al’ummar duniya kai wa biliyan 9 har zuwa shekarar 2037.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.