Isa ga babban shafi
TARON G20

Shugabannin G20 na kokarin ceto duniya daga rugujewa saboda yakin Ukraine

Shugabannin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya G20 sun bude babban taronsu wannan Talata a tsibirin Bali na kasar Indonessia, inda mai masaukin baki na neman hadin kai da kuma daukar kwararan matakai don daidaita tattalin arzikin duniya duk da rashin jituwar da ake fama da ita kan yakin Ukraine.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden da takwaransa na China Xi Jinping yayin taron G20 a kasar Indonessia, 14/11/22.
Shugaban kasar Amurka Joe Biden da takwaransa na China Xi Jinping yayin taron G20 a kasar Indonessia, 14/11/22. AP - Alex Brandon
Talla

A jawabinsa na bude taron shugaban kasar Indonesia Joko Widodo mai masaukin baki, yace basu da wani zabi a halin da duniya ke ciki face bukatar hadin gwiwa don ceto duniya daga rugujewa.

Widodo yace ya zama wajibi kasashen G20 su samar da hanyoyin farfado da tattalin arziki, yana mai cewa bai kamata su kasance silar rarrabuwar kawunan duniya tare da kaucewa fadawar duniyar cikin wani yakin cacar baka.

G20

G20 da ta hada da kasashe daga Brazil zuwa Indiya, Saudiya da Jamus, na da sama da kashi 80 cikin 100 na yawan kayayyakin da ake samarwa a duniya, kashi 75% na cinikin kasa da kasa da kuma kashi 60% na al'ummarta.

Wata kyakkyawar alamar murmurewar duniya da aka gani tun a jajibirin taron ita ce ganawar da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi da takwaransa na China Xi Jinping na tsawon sa'o'i uku, inda shugabannin biyu suka yi alkawarin karfafa cudanya da juna duk da bambance-bambance da dama dake tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.