Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci yafewa kananun kasashe basukan da ke kansu

Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da wani kudirin saukaka bashi ga matalautan kasashe da marasa karfin tattalin arziki 52 a wani yunkuri na rage musu nauyi dai dai lokacin da tattalin arzikin su ke fama da tarin matsaloli.

Achim Steiner, shugaban hukumar UNDP.
Achim Steiner, shugaban hukumar UNDP. AP - MARTIAL TREZZINI
Talla

Majalisar ta mika wannan bukata ne kanwaki 2 gabanin taron ministocin kudin kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki da India za ta karbi bakonci, inda ta ce ta hakan ne za a saukakawa kasasshen don su iya tafioyar da sabbin tsare-tsaren da zai habaka tattalin arzikinsu.

Shugaban shirin bunkasa kasashe na Majalisar Dinkin Duniya UNDP Achim Steiner ya ce kashi 40 na kasashe matalauta ko kuma masu tasowa na cikin matsanancin yanayi saboda basukan da ke kansu, yayinda wasun su basa iya tafiyar da sha’anin mulki saboda irin wadannan basuka.

A cewarsa ta hanyar sassauta musu basukan ko kuma yafe musu baki daya ne kadai za a iya ganin farfadowarsu daga mashasshar da tattalin arzikinsu ya shiga.

Shugaban na UNDP ya bayyana cewa kasashe da dama na fuskantar barazanar durkushewa tun bayan mummunar illar da covid-19 ta yiwa tattalin arzikinsu 2020 ga kuma tarin bashin da ke kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.